1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jonathan ya yi maraba da tayin Amirka

May 6, 2014

Kasar Amirka za ta tura jami'an tsaro da kayayakin aiki don tallafa wa Najeriya ceto 'yan matan nan da aka yi garkuwa da su fiye da makonni uku a garin Chibok.

https://p.dw.com/p/1BulT
Nigeria Präsident Goodluck Jonathan Beerdigung Autor Chinua Achebe
Hoto: Pius Utomi ekpei/AFP/Getty Images

Wannan amincewar da tayin tura jami'an tsaron Amirkan da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi, ya zo bayan jerin zanga-zanga da zaman dirshan da ake yi a sassa daban daban na Najeriya don yin matsin lamba ga hukumomin kasar da su kara azama wajen kubutar da 'yan matan daga hannun 'yan bindigar kungiyar Boko Haram da suka sace su. Da ma dai an yi ta yin kira ga shugaban Najeriyar a ya nemi taimako daga ketare kasancewa lamarin na son ya gagari hukumomin kasar ta Najeriya.

A kan wannan batu kuwa na tabarbarewar tsaro a arewacin kasar, a wannan Talata wata tawagar shugabannin yankin arewa maso gabacin Najeriya sun gana da shugaba Jonathan inda suka nuna masa rashin jin dadinsu game da sako-sako da mahukuntan na Abuja ke yi na magance matsalar.

Taron tattalin arzikin duniya kan Afirka

Li Keqiang
Hoto: Getty Images/Alexander F. Yuan

Hakan dai na zuwa a daida lokacin da kuma Najeriya ke karbar bakoncin babban taron kasashen duniya kan batun tattalin arziki da zai gudana a Abuja, lamarin da ya sanya sauya yanayin harkoki a birnin musamman zirga-zirgar jama'a.

Wannan taro mai muhimmanci da ma zama abin alfahari ga mahukuntan Najeriyar daukacin harkokin birnin Abujan sun sauya inda a ko-ina ka duba alamu na zahiri na nuna cewa akwai muhimmin taro da zai gudana a birnin.

Mawallafa: Ubale Musa / Uwais Abubakar Idris
Edita: Mohammad Nasiru Awal