1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jordan ta kori jakadan Siriya da ke kasar

May 26, 2014

Mahukuntan Jordan sun sallami jakadan Syria da ke kasar saboda abinda suka kira barazanar da zamansa ke yi ga kasar baki daya.

https://p.dw.com/p/1C7IN
Jordanien Syrien syrische Botschaft in Amman
Ofishin jakadancin Siriya da ke JordanHoto: KHALIL MAZRAAWI/AFP/Getty Images

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Jordan din Sabah al-Rifai ya ce gwamnatin kasar ta yanke wannan shawar ce bayan da jakadan na Siriya ya mika wasu muhimman bayanai na sirri ga manema labarai wanda Jordan din ke cewar hakan ya saba ka'aida ta aiki diflomasiyya.

Wannnan dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan da jakadan na Siriya ya soki mahukuntan Jordan dangane da yunkurin da ya ce suna yi na hana gudanar da zaben shugaban kasar Siriya a ofishin jakadancinsu da ke Jordan din.

Tuni dai kafar watsa labaran gwamnatin Siriya ta yi Allah wadai da wannan mataki na Jordan har ma ta ce gwamnatin Siriya ta sallami jakadan Jordan din da ke kasarta a wani mataki na ramuwar gayya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar