Jos: Musulmi da Kiristoci na siyasa a tare
December 22, 2017Yanzu haka dai akwai ire-iren waddan nan kungiyoyi da dama wadanda suke shiga harkokin siyasa mai makon yadda a baya ake amfani da su wajen yin bangar siyasar. Mr Lemark Peter shi ne babban daraktan kungiyar matasa da ka kira Yes 2019 wadda kungiya ce ta siyasa, ya ce sun hado matasan Musulmi da Kirista ne cikin dandali guda don rika cudanya da juna a siyasance.
A shekarun baya dai matasan daga bangarorin biyu sun yi ta kai ruwa rana tsakanin su musamman ma a lokutan zabe, to sai dai yanzu sun ce sun gano 'yan siyasa na amfani da su ne kawai wajen salwantar da rayukan junansu don kawai su sami shugabanci. Dalili kenan da ya sa suka kafa kungiyoyin da za su rika taimakon juna maimakon bangar siyasa. Malam Bala Buswat wani matashi ne daga karamar hukumar kanam ya ce su kan samar wa 'yan uwansu matasa sana'o'i ta hanyar wadannan kungiyoyi da suke kafa wa.
Yayin da Najeriya ke tinkarar babban zabe a shekarar 2019, shugabanin matasan na Filato sun hakake cewar za su isar da wannan kyakyawar manufa tasu ga shauran yan'uwansu matasa da ke wasu jihohi musamman ma jihohin da a kan fuskanci tashe-tashen hankula na addini a cewar Mr Polycarp Jurbe mataimakin daraktan kungiyar siyasa ta Yes 2019 a jihar Filato.