Juba: Yarjejeniyar zaman lafiya ta shiga rudani
April 18, 2016Talla
An sake dage ranar da jagoran adawa a Sudan ta Kudu Riek Machar zai koma Juba babban birnin kasar don aiwatar da shirin zaman lafiya da aka kulla da shugaba Salva Kiir. Yanzu dai nan da sa'o'i 24 ne ake sa ran Machar zai isa birnin na Juba kamar yadda mai magana da yawun 'yan adawar ya bayyana a ranar Litinin din nan.
Da yake jawabi ga manema labarai a filin tashi da saukar jiragen sama na Juba William Ezekiel ya ce an dage zuwan jagoran nasu saboda dalilai na rashin kammala wasu tsare-tsare.
Ba da dadewa ba ne dai Machar ya zo garin Pagak da ke a kan iyaka a kasar ta Sudan ta Kudu bayan ya baro kasar Habasha. An dai tsara cewa da zarar ya isa birnin na Juba za a rantsar da shi a matsayin mataimakin shugaban kasa.