Lafiya
Kara hubbasa na yaki da Maleriya
November 19, 2018Talla
Hukumar Lafiya ta Duniya ta nuna damuwa da sako-sako kan yaki da cutar zazzabin cizon sauro a kasashe da dama galibi na nahiyar Afirka inda rayuka ke ci gaba da salwanta.
Bayan shafe shekaru na samun nasara kan yaki da cutar zazzabin cizon sauro, yanzu akwai tafiyar hawainiya kamar yadda jami'in kula da yakin da cutar na Hukumar Lafiya ta Duniya Pedro Alonso ya bayyana bayan fitar da rahoton shekara ta 2018 a wannan Litinin.
Cutar zazzabin cizon sauro tana ci gaba da illa a nahiyar Afirka, inda a shekara ta 2017 kashi 70 cikin 100 na mutuwa da aka samu sakamakon cutar a nahiyar ne, kuma kasashe da ke sahun gaba sun hada da Kamaru, Najeriya da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango - sai kuma Indiya daga wajen nahiyar Afirka.