Kakakin Shugaba Trump ya yi murabus
July 21, 2017Kakakin shugaba Trump na Amirka Sean Spicer ya yi murabus daga kan mukaminsa a wannan Jumma'a bayan watannin shida kacal a fadar white House.
Kafofin yada labarai a kasar ta Amirka sun bayyana cewa Sean Spicer dan shekaru 45 wanda kuma ke daya daga cikin mutanen da ke da kima a idon Amirkawa daga cikin mukarraban Shugaba Trump, ya aje aikin nasa ne bayan da shugaba Trump ya nada Anthony Scaramucci a matsayin sabon daraktan kula da harakokin sadarwarsa domin maye gurbin tsohon daraktan wanda shi ma ya yi murabus ne daga kan mukaminsa a watan Mayun da ya gabata bayan watanni uku kadai na aiki da Shugaba Trump.
A makonni baya bayan nan dai kakakin na Shugaba Trump na shan suka maigidan nasa sakamakon kura-kuran sadarwa da aka yi ta samu a fannin zartarwar kasar musamman wajen neman kare Shugaba Trump a game da binciken da babban alkalin kasar Robert Mueller ya kaddamar kan rawar da aka zargin Rasha ta taka a yakin neman zaben Shugaba Trump a shekarar bara.