Kalaman Saraki kan IPOB ya tada kura a majalisa
September 26, 2017‘Yan majalisar dattawan Najeriyar dai sun dauki lokaci mai tsawon gaske suna zaman sirri abin da ba'a saba gani ba a rana ta farko ta dawowa daga dogon hutun da ake sa ran jawabi na maraba daga shugaban majalisar. Tun kafin dawowar majalisar dai akwai wakilanta da dama da ke kumfar baki da ma nuna bacin ransu a kan kalaman da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya yi na nuna rashin amincewa da ayyana kungiyar masu fafutikar kasar Biafra ta IPOB a matsayin kungiya ta ‘yan ta'adda.
Bayanai sun nuna cewa sun amince da dorewar Najeriya a matsayinta na kasa daya al'umma daya ba tare da bada kafa ga duk wata kungiya mai kokarin ballewa ba. To sai dai ga kakakin majalisar dattawa Sanat Aliyu Sabi Abdullahi ya ce akwai bukatar fahimtar kalaman da shugaban majalisar ya yi.
A majalisar wakilan Najeriyar ma dai wannan batu ne ya dauki hankali sosai a tsakanin ‘yan majalisar, inda a jawabin maraba ga ‘yan majalisar shugabanta Hon. Yakubu Dogara shi ma ya jadada hatsarin bari ko bada kafa ga duk wata kungiya da ke furta kalamai na batanci ga yanayin zaman lafiya na Najeriyar.
Duk da cewa ta kaisu ga gabatar da kuduri na musamman a kan wannan batu da ke kama hanyar zama doka da za'a hukunta duk wanda aka samu da furta kalamai na batanci, amma ga Hon. Ahmed Baba Kaita ya ce basu yarda da kalaman da Sanata Bukola Saraki ya yi a game da kin amincewa da ayyana kungiyar IPOB ta ‘yan ta'adda ta yi ba.
Duk da kokari na yiwa tufkar hanci a tsakanin ‘yan majalisar dattawan Najeriyar, a bayyane take cewa kokari na karo da juna a kan ayyukan bangaren zartaswa da na majalisu masu dokoki na zama abin da ke sanya nunawa juna ‘yar yatsa a kan batun.