1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen fadin albarkacin baki a Zimbabuwe

Yusuf BalaMay 25, 2016

A kasar Zimbabwe gidajen harkokin wasanin kwaikawayo ne yanzu haka suka rage wajen bayyana fadar albarkacin baki saboda barazanar gwamnati.

https://p.dw.com/p/1Iu2w
Simbabwe Harare Theatre in the Park​
'Yan wasan kwaikwayo a birnin Harare na baje fasaharsu ta fadin albarkacin bakiHoto: DW/P. Musvanhiri​ ​

Wasan kwaikwayo da wannan salo na fadin albarkacin baki ya bullo ne sakamakon irin yadda shugaba Robert Mugabe ya yi nuni da cewar Zimbabuwe ta yi asararbiliyan 15 na kudaden zinayira a shekaru 10 da suka wuce a yayin wata hira ta manema labarai lokacin bikin cikarsa shekarun sa 92 a duniya, wannan shi ne ma dalilin da ya sanya Silvanos Mudzvova ya ji ya kamata ace ya fito domin bayyana irin yadda kasar ke yin wasarairai da dukiyar kasar.

"Wannan aiki na ne kuma da wannan nake samun kudade, ya zama wajibi na yi aikina domin fadakar da kasa, idan muna jin tsoro yin hakan to waye zai gabatar da sakonni ga mutane ba mu da wani zabi illa mu yi haka."

Yancin fadar albarkacin baki a kasar Zimbabuwe abu ne tabbatacce a kudin tsarin mulkin kasar to amma yin sa haramun ne, masu wasanin kwaikwayo ko rubuce rubuce ba sa iya samun damar baje kolinsu wajen magana irin san ransu ga shugabanin kasar.

Mugabe feiert 92. Geburtstag
Shugaba Mugabe da matarsa a lokacin bikin cikarsa shekaru 92 da haihuwaHoto: picture-alliance/dpa/A. Ufumeli

Daraktan cibiyar baje kolin wasanin Davis Guzha ya yi namijin kokari don ceto cibiyar wajen fadar albarkacin bakinta.

"Akwai bukatar diga ayar tambaya ga razana ta hanyar tambaya ba tare da jin dar dar ba ta yin tambayar ya ya kake ganin abu kaza kuma ya ya ka ke ganin yadda ka ke gudanar da abubuwa".

A kasar Zimbabbwe dai kamar sauran kasashe a Afirka hukumar tace fina finani na yin tankade da rairaya kafin a bada damar sakin faya fayen Elvas Mari shi ne darakatan hukumar.

"Harkokin rubuce rubuce da wasanin kwaikwayo ababe ne masu girma kamar yadda ka sani suna iya sauyawa mutane tunaninsu, don haka dole ne mu kasance a cikin shiri a koda yaushe."

Yanzu haka dai gwamnatin kasar Zimbabuwe na kallon wasu finafinan wasanin kwaikwayon a matsayin sun saba ka'ida to amma wadanda al'amarin ya shafa na ci gaba yin iya bakin kokari.