Kalubalen ilimin mata 'yan gudun hijira a duniya
March 7, 2018Talla
Rahoton da aka fitar a jajibirin ranar mata na duniya, ya ce wannan matsala ta fi kamari ne a tsakanin 'yan gudun hijira da suka bar gidajensu sakamakon rikice-rikice a sassan duniya, kamar yadda babban jagoran hukumar kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ta HCR, Filippo Grandi ya sanar.
Rahoton ya ce rabin yara 'yan gudun hijira miliyan 3.5 da ke a fadin duniya, ba su samun zuwa makaranta ba, wanda kuma matsalar an fi samunta ne a makarantun sakandare zuwa na gaba da sakandare kamar yadda rahoton na HCR ya sanar, inda ya ce a cikin kasashe irin su Kenya, da Habasha, lamarin ya fi kamari.