Kama manyan jami'an gwamnatin Gambiya game da miyagun ƙwayoyi
March 9, 2010An kama wasu manyan jami´an gwamantin Gambiya bayan da aka zargesu da marar hannu a safarar miyagun ƙwayoyi da ƙasar ta fara ƙaurin suna akai. Hapsoshin soja da na yan sanda da ma dai wani tsohon minista na daga cikin manyan jami´ai 11 da ke tsare a halin yanzu a birnin Banjul. Shugaba Yahya Jammeh ya sha alwashin sa ƙafar wando guda da duk waɗanda ke ruwa da tsaki wajen taimaka cinikin faudar ibilis da sauran miyagun ƙwayoyi samun gindin zama a wannan ƙasa. Shugaban hukamar yaƙi da miyagun ƙwayoyi da kuma mataimakinsa da kuma speto janar na yan sanda na scikin ayarin wadanda aka tuɓe tare da tasa ƙeyarsu i zuwa kurkuku.un shiga hannun jami´an tsaro sakamakonbayan da gwamata tsafake wasu manayan jami´anta bisa zargin safarrar miyagun ƙwayoyi.
Mawallafi: Mouhammadou Awal Edita: Zainab Mohammed