Kamaru: Biya ya fara sabon wa'adin mulki
November 6, 2018Talla
Da ya ke gabatar da jawabi a yayin shagalin bikin rantsuwar da kakakin majalisar Dokokin kasar Cavaye Yeguie Djibril ya jagoranta, Shugaba Biya ya jaddada aniyarsa ta maido da martabar kasar. Wannan dai shi ne wa'adin sa na bakwai a shugabancin kasar. Sama da mutane dubu 300 daga cikin al'ummar kasar ne ke zaune a dazuzuka cikin yunwa a halin yanzu sakamakon gujewa rikicin 'yan aware masu neman kafa kasar Ambazoniya daga cikin Kamarun.