1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ba da umurnin sakin 'yan awaren Kamaru

Gazali Abdou Tasawa
December 13, 2018

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya ba da umurnin dakatar da tuhumar da ake yi wa wasu masu fafutika na yankin Anglophone na kasar su 289 wadanda ake tsare da su

https://p.dw.com/p/3A4Nt
Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Warnand

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a wannan Alhamis da a gidan radiyo na kasar ya karanto, ta ce shugaban kasar ya dauki wannan mataki ne domin bai wa matasan da ke dauke da makamai damar mika makaman nasu da ba da hadin kai ga kwamitin da aka kafa domin karbe makamai daga hannun 'yan awaren da kuma samar masu da aikin yi.

Daruruwan 'yan awaren yankin Anglophone na kasar ta Kamaru ne dai ke kargame a gidajen kurkukun kasar dabam-dabam da suka hada da jagoran 'yan awaren Julius Sisiku Ayuk Tabe wanda hukumomin kasar ta Kamaru ke zargi da laifin ta'addanci da kuma tawaye.