A kwanakin baya ne majalisar dokokin jihar Kano dake Tarayyar Najeriya ta kafa dokar hana bara da kuma tanadar hukunci mai tsauri ga duk almajirin da ya ki bin wannan doka. A yanzu haka dai dokar ta fara aiki gadan-gadan inda tuni aka kaddamar da fara kame almajiran da suka fito suna bara a kan titunan jihar.