Kamfanin Facebook ya fara tambayar Jin ra'ayin jama'a
April 3, 2018Talla
Ma'abota amfani da Facebook na cigaba da bayyana ra'ayoyin su kamar yadda Shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ya bukata,lamarin da ya ba wasu daga cikin al'umma damar bayyana gamsuwar su ,a hannu guda kuma wasu na neman kamfanin ya yi gyara a guraren da ake tuhumar sa da sakaci.
A halin yanzu Facebook na fuskantar zarge-zargen da suka hada da amfani da bayanan jama'a ba tare da izinin su ba don aiwatar da ayyukan zabe a wasu kasashen da kuma rura wutar rikicin kabilanci da addini.
A nasa bangaren shugaban kamfanin ya bayyana burin sa na wannan shekara da kawo gagarumin gyara a Facebook.