Lufthansa da abokan huldarsa sun soke jigila zuwa Isra'ila
April 19, 2024Kamfanin sufurin jiragen sama na Lufthansa na nan Jamus, ya sanar da cewa shi da abokan huldarsa na Swiss Airlines da Austrian Airlines, sun dakatar da jigilar fasinjoji zuwa Isra'ila, sakamakon tashin hankalin da yankin Gabas ta Tsakiya ke fuskanta.
Karin bayani:Yajin aiki ya tilasta rufe filin jirgin saman Frankfurt na Jamus
Mai magana da yawun kamfanin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus DPA cewa, a Juma'ar nan ma sun soke jigilar wasu jiragensu 4 da a baya aka tsara cewa za su je Isra'ila da safiyar Asabar.
Karin bayani:Sabuwar takaddama tsakanin Jamus da Rasha
Kafafen yada labaran Amurka sun rawaito cewa Isra'ila ta kai wa Iran harin makami mai linzami, to amma babu rahoton wata asara da harin ya haddasa.
A karshen makon jiya ne dai Iran ta kai wa Isra'ila hare-hare sama da 300 na makamai masu linzami da jirage masara matuka, wanda Amurka da sauran kawayenta suka taimaka mata wajen kakkabo mafi akasarinsu.
A wani labarin, shi ma kamfanin sufurin jiragen sama na kasar Poland, ya sanar da soke zirga-zirgarsa zuwa birnin Tel-Aviv na Isra'ila da Beirut na Lebanon.