Kanada za a tusa keyar jami'an diflomasiyya 41 na Indiya
October 20, 2023Talla
Rikicin ya biyo bayan kisan da aka yi a watan Yunin da ya gabata na wani shugaban 'yan awaren Sikh a kasar Canada. Hardeep Singh Nijjar, wanda aka kashe a kusan yammacin birnin Vancouver , dan gwagwarmaya ne mai fafutukar kafa Khalistan, yankin Sikh mai cin gashin kansa a arewacin Indiya.Tun farko a cikin watan satumba da ya gabata firaministan Kanada Justin Trudeau ya ce jami'an leken asirin Indiya na da hannu cikin wannan kisan, wanda ya haifar da rikicin diflomasiyya tsakanin Kanada da Indiya, sai dai Indiyar ta musunta zargin.