1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kano: Hukuncin rajamu kan aikata fyade

Abdullahi Tanko Bala
August 12, 2020

Wata babbar kotun shariar musulunci da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta yanke hukuncin Rajamu kan wani magidanci mai shekaru 70 bisa samun sa da yi wa yarinya 'yar shekaru 12 fyade.

https://p.dw.com/p/3grZ8
Symbolbild Gericht Gesetz Waage und Hammer
Hoto: Fotolia/Sebastian Duda

Magidancin mai suna Mati Audu ya amsa cewa ya aikata wananan laifi inda kuma daga nan mai sharia Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya yi amfani da furucin mai laifin wajen yanke masa hukuncin kisa ta hanyar jefewa.

Mati Audu bai sami lauyan da zai kare shi ba a gaban kotun yayin hukuncin da aka zartas masa to amma lauyan gwamnati Barrister Zaharadden Mustapha ya ce hukuncin yayi dadi dai domin zai zama izina ga masu irin wannan laifi na fyade,

Hukuncin na rajamu ya zo a wani yanayi da aka dade ba'a ga irinsa ba, saboda ba kasafai ake yi wa mutane hukunci da rajamu akan abin da ya shafi fyade ba.

A kwanannan ma sai da wata babbar kotun musulunci ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wani sha'iri da aka samu da laifin yin kalaman batanci ga manzon Allah.