Najeriya: Za a kara jibge sojoji tsakanin Kaduna da Abuja
November 25, 2021An dai share mafi yawa na wannan mako dai ana daukar dai-dai kan babbar hanyar da ta hade Abuja da ke zaman cibiyar mulkin tarrayar Najeriya da kum a Kaduna da ke arewacin kasar. Kusan daukaci na wannan mako dai babban titin na Kaduna zuwa ga Abujar ya zama tarkon mutuwar da ya kai ga asarar manya da kanana na 'yan kasar daga hannu na barayin dajin Abin kuma da ya tada hankalin al'ummar arewacin kasar da ke mata kallon babbar gadar hade sassan arewacin kasar da kudancinta, da ita kanta gwamnatin da ke kara shiga tsaka mai wahalar gaske. A cikin karatun na barawo da mai takama da kayan gado dai manya na jami'an tsaron kasar da shugabanni na siyasa dai sun yi wata ganawar sirri da nufin tinkarar matsalar dama jerin matsalolin tsaron da ke sassa dabam-dabam cikin Najeriyar.
Kara daukar matakan tsaro gabannin bukukuwan Sallah Kirismeti
Kuma an kare taron tare da masu mulki na kasar yanke hukuncin kara jibge jami'an tsaro kan babar hanyar dama sauyin tsari na tsaro a karatowa na bikin kirismeti a kasar a fadar rauf Aregbesola da ke zaman ministan cikin gidan kasar.“ An bai wa 'yan sanda da sauran jami'an tsraon umarnin hada karfi domin karin shawagi da tinkarar 'yan laifi. Ba wai kawai a hanyar Abuja zuwa Kaduna ba. Eh an duba batun na Abuja zuwa Kaduna a kansa, amma kuma mun yi la'akari da cewar ana kara kusantar bukukuwa na Kirsimeti da karshe na shekara.