Hadin kai domin taimaka wa rayuwar 'yan gudun hijira
June 20, 2019Ranar 'yan gudun hijirar ta bana ta zo a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun rigingimu da ke raba dubban mutane da iyalai daga matsugunansu domin komawa wuraren da suke gani tudun mun tsira amma kuma suke shiga mawuyacin hali. Wasu sabbin alkaluma da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun nuna cewa kimanin mutane miliyan 71 da aka tilastawa ficewa daga gidajensu saboda rikici da yake-yake a fadin duniya. Alkaluman sun nuna cewa a duk minti daya ana raba mutane a kalla 20 daga matsugunansu ko kuma duk dakika ana korar mutum daya daga matsuguninsa a karshen shekarar da ta gabata.
A shiyar Arewa maso gabashin Najeriya ana samun karuwar ‘yan gudun hijira a kullum saboda hare-haren da bangarorin mayakan Boko Haram ke kaiwa inda ake ci gaba da samun kalubalen a ayyukan jin kai. Wadanan 'yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali inda yunwa da cutuka ke hallaka wasunsu duk da tallafi da agajin da gwamnatoci da wasu Kungiyoyin agaji na ciki da wajen Najeriya ke bayarwa.
A cewar hukumar bada agajin gaggawa ta jhar Borno Alhaji Usman Kachalla, hukumomi da sauran kungiyoyin agaji na yin baki kokarin su domin samar da abinci da sauran kayayyakin more rayuwa ga ‚yan gudun hijirar. A irin wannan rana Majalisar Dinkin Duniya na karfafa gwiwar jama'a su hada kai da gwamnati domin magance matsalolin 'yan gudun hijirar maimakon zubawa gwamnati da sauran kungiyoyi ido.