Karfin soja da makaman Koriya ta Arewa
A shekarun baya duniya ba ta dauki karfin sojan Koriya ta Arewa da mahimmanci ba amma bisa nasarar gwajin makami mai linzami da ke cin dogon zango na nuna cewa karfin sojan Pyongyang na habaka.
Rundunar soja mai girman gaske
Baya ga habaka makamai masu linzami da nukiliya, Koriya ta Arewa na da rundanar soja mai girma da ta kunshi soja 700,000 da ke bakin daga. Akwai kuma wasu miliyan hudu da rabi da ke cikin shirin ko ta kwana. An yi kiyasin yawan sojan Koriya ta Arewa ya ninka na makobciyarta Koriya ta kudu har sau biyu.
Karfi ta ko ina
Bisa lissafin da aka yi na karfin makamai a duniya na shekara ta 2017, Koriya ta Arewa na da jiragen yaki 458 da takokin yaki 5,025 da kuma, jiragen ruwa da ke tafiya karkashin ruwa guda 76. Kasar na da yawan sojoji fiye da miliyan 5. Wannan hoton da aka dauka a 2013 na nuna shugaba Kim Jong Un na bada umarnin kan rokokin da za su auna Amirka da Koriya ta Kudu.
Kasaitaccen bikin nuna karfin soja
A duk shekara dubban sojoji na yin maci a tsakiyar Pyongyang babban birnin Koriya ta Arewa. A kan fara shirye-shiryen bikin watanni da dama kafin gudanar da shi, inda a kan zabi ranar karrama jam'iyya mai mulki ko kuma tunawa da iyalan jogoran kasar Kim Jong Un.
Gwajin nukiliyan a Pyongyang ana kirga biyar kan a sake bomb din
Makamin mai raza nahiya da aka sani da ICBM an yi imanin cewa ci gabane ga Koriya ta Arewa. Duk da jerin takunkumin da ke kanta, Pyongyang ba ta boye muradinta na mallakar nukiliya ba. Bayaga gwajin makamai masu linzami da ta saba yi. Koriya ta Arewa sau biyar tana gwajin makaman nukiliya, a bara sau biyu tana yi. Kasar ta yi ikirarin makaman da ta gwada abaya-bayannan ana iya harba roka da shi
Makiya daga kowanne bangare
Baya ga kasar Amirka, Pyongyang na daukar Koriya ta kudu da Japan a matsayin manyan abokin gaba. Koriya ta Arewa ta yi amfani da rawar daji da sojan Amirka ke yi a yankin a matsayin wata dama wajen fargar da 'yan kasarta, inda ta yi ikirarin cewa rawar dajin wani shiri ne na mamaye kasar da aka kitsa.
Ko hakurin Amirka ya kusan karewa?
A martaninsu gwajin makamin mai linzami da ke cin nisan zango da kuma nuna karfin soja, Amirka da Koriya ta Kudu sun gudanar da wani atisaye inda suka harba makamai masu linzami wato ATACMS da Hyunmoo Missile II. A watan Aprilu Amirka ta tura jirgin ruwa mai dakon jiragen yaki zuwa tsibirin Koriya da nufin a wani mataki na lura da abin da ke faruwa a Koriya ta Arewa.