1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kharim Khan zai jagoranci kotun ICC

Abdourahamane Hassane
June 16, 2021

A nada lauyan nan dan Kasar Birtaniya Karim Khan a matsayin babban alkali mai shigar da kara na kotun kasa da kasa wato ICC ko CPI da ke a birnin Hague.

https://p.dw.com/p/3v2jV
Bildkombo Internationaler Strafgerichtshof Fatou Bensouda und Nachfolger Karim Khan

Karim Khan ya maye gurbin Fatou Bensouda 'yar kasar Gambiya wacce ta kwashe shekaru 12 a kan matsayin. Khan zai fara aiki ne da manyan ayyuka a gabansa na kaddamar da bincike a game da rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinu da batun  Afghanistan da kuma Philipins.