1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin albashi ga 'yan majalisar dokokin Kenya

May 29, 2013

Duk da cewar 'yan majalisar dokokin Kenya na sahun farko a duniya wajen yawan albashi, sun sake kara wa kansu albashin.

https://p.dw.com/p/18h6k
Protestors carry placards as they participate in a demonstration against lawmakers' salary demands near parliament buildings in the capital Nairobi, May 14, 2013. Kenyan police in riot gear fired teargas and water cannons on Tuesday to disperse about 200 protesters gathered outside parliament to demonstrate against lawmakers' salary demands. REUTERS/Thomas Mukoya (KENYA - Tags: SOCIETY CIVIL UNREST POLITICS)
Hoto: Reuters

Hukumar kayyade albashi da alawus-alawus na ma'aikatsn gqwamnati da kuma na 'yan siyasar kasar Kenya ce dai ta turawa majalisar dokokin kasar bukatar rage yawan albashin da kowane dan majaolisa ke karba, daga kimanin kudi dalar Amirka dubu 126n da mambobin tsohuwar majalisar dokokin ke karba, ya zuwa dalar Amirka dubu 78 bisa abinda hukumar ta ce albashin ya zarta tunani.

Hakanan hukumar kayyade albashin ta kafa hujjar cewar, duk da cewar Kenya na sahun farko wajen jerin kasashen duniya da ke fama da talauci, da kuma koma bayan tattalin arziki, amma kuma 'yan majalisar dokokin kasar sun zarta na kasar Faransa alal misali, wadda ke da karfin tattalin arziki.

Sai dai a maimakon rage albashin, sai kwatsam 'yan majalisar dokokin suka kara shi, abinda kuma ya janyo martani daga kungiyoyin fararen hula da masana shari'ah a kasar.

Protestors parade pigs and pig's blood as they participate in a demonstration against lawmakers' salary demands outside parliament buildings in the capital Nairobi, May 14, 2013. Kenyan police in riot gear fired teargas and water cannons on Tuesday to disperse about 200 protesters gathered outside parliament to demonstrate against lawmakers' salary demands. The words written on the pigs are the names of the legislators. REUTERS/Thomas Mukoya (KENYA - Tags: SOCIETY POLITICS CIVIL UNREST ANIMALS)
Aladu da zubar da jini a harabar majalisar dokokin KenyaHoto: Reuters

Martanin kungiyoyi ga karin albashi ga 'yan majalisa

Eric Mutua, shugaban kungiya lauyoyi ta kasar Kenya, ya ce zai kalubalanci matakin majalisar dokokin na yin watsi da bukatar hukumar kayyade albashin na su a gaban kotu, domin a ganinsa bai dace majalisar ta sa kafa ta shure bukatar ba.

Sai dai kuma Koigi Wamwere, tsohon dan majalisar dokokin kasar ta Kenya, ya ce akwai fa dalilan da suka sanya 'yan majalisar karkata zuwa ga wannan ra'ayin:

Ya ce "A shirin zaben da matsalar kabilanci da na cin hanci da rashawa suka dabaibaye, tilas ne idan kana bukatar majalisar dokokin da mambobinta za su gamsu da albashinsu, ka hana 'yan mazabunsa nem,an cin hanci da rashawa. Kazalika, mutane na jiran gwqamnati ta samar musu da ababen more rayuwa kamar hanyoyi da biyan kudaden asibiti da kuma na makarantun da dai sauransu. Irin wadannan abubuwa suna taimakawa gaya wajen jefa 'yan majalisar dokoki cikin matsalar cin hanci."

Zargin ruruta matsalar cin hanci a kasar ne yasa dubbannin 'yan Kenya gudanar da jerin zanga-zanga a harabar majalisar dokokin, in da a lokacin daya daga cikin irin jerin gwanon ne suka saki aladu a bakin babbar kofar shiga majalisar dokokin, domin nuna cewar 'yan majalisar mahandama ne.

A tsokacin da yayi dangane da cece-kucen da batun karin ya janyo kuwa Koigi Wamwere, tsohon dan majalisar dokoki kasar ta Kenya, ya ce majalisar na son jefa kasar ne cikin rudani:

Ya ce "A halin da muke ciki yanzu, kowa ma zai bukaci samun albashi mai tsoka. Gwamnoni za su nemi samun albashi mai girma. Hakanan malaman makaranta. Kai hatta marasa aikin yi ma za su nemi hanyar satar kudi daga gwamnati. Kasar za ta kara tsunduma cikin matsalar cin hanci da rashawa kenan."

Kenia Kenyatta inoffizieller Wahlsieger
Shugaba Uhuru Kenyatta na KenyaHoto: Reuters

Rage albashin shugaban kasar Kenya

Dama dai hukumar kayyade albashin ma'aikata da jami'an gwamnati a Kenya ta rage albashin shugaban kasaa daga dalar Amirka dubu 340 ya zuwa dala dubu 185 a kowace shekara, a kasar da mafi karancin albashi ke zama dala 1,500 a kowace shekara.

Hukumar ta ce bisa la'akari da sabon yanayin da Kenya ta samu kanta a ciki na zaben sabbin gwamnoni 47, da 'yan majalisar dattijai 67, wanda yasa yawan 'yan majalisar dokokin karuwa daga 22 zuwa 349, karfin aljihun gwamnatin ba zai iya daukar nauyin hakan ba. Akan hakane shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya bukata 'yan majalisar dokokin da su jira tukuna sai tattalin arzikin kasar ya bunkasa gabvannin su yi batun karin albashinsu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou