Najeriya: Karin kafafen yada labarai
September 29, 2021Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne dai ya sanya hannu, domin yarjewa wadanda ke da bukatar kafa sababbin tashoshin radiyo da talabijin din masu zaman kansu a kasar kimanin har 159. Wadanda gwamnatin ta sahalewa bude tashoshin talabijin da radiyon dai, sun hadar da kamfanoni masu zaman kansu da manyan makarantu kamar jami'o'i da kwalejojin kimiyya da fasaha da kuma wasu yankunan da kan bude gidajen radiyo na al'umma wato Community Radio.
Za a iya cewar kafafen yada labarai na talabijin da radiyo na da kalubale babba, wajen ganin sun bi ci-gaban fasahar zamani ta kafar Internet wato kafafen sada zumnta na zamani, inda akasari ake samun labaran bogi da ke cin karensu babu babbaka. Mafi yawan al'umma dai na dogara da kafafen, wajen ji ko ganin labarai. Wannan ya sa da daman kafafen yada labarai na talabijin da radiyo a Najeriyar, samarwa kansu dandalin yada shirye-shiryensu. Babban dai aiki ga Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa a Najeriyar wato NBC, shi ne tabbatar da cewar wadannan kafafen yada labaran na bin dokokin kasa da ka'idojin kafa su kuma abin da mutane da dama ke fatan ganin NBC din ta dage a kai ke nan.