Karin takunkumi kan Koriya ta Arewa
January 7, 2016Talla
Kakakin majalisar dokokin Amirka Paul Ryan ya ce akwai yiwuwar majalisar ta tattauna kan kakabawa Koriya ta Arewa karin takunkumi bayan da ta yi gwajin makamin nukiliya.
Ryan ya ambata hakan ne dazu, sai dai kuma bai yi karin haske kan batun ba, amma jagorar yan majalisar wakilai ta jam'iyar Democrat Nancy Pelosi ta ce akwai yuwuwar kila a yi zaman a farkon mako mai kamawa.
Kasashen duniya ciki kuwa har da China wadda ke dasawa da Koriya ta Arewan sun yi Allah wadai da gwajin makamin na kare dangi da ta yi wanda ake ganin barazana ce ga zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya.