Karon batta tsakanin Ingila da Jamus
Wasa tsakanin Ingila da Jamus a gasar cin kofin Turai a Wembley na da dadadden tarihi. Ba gaskiya ba ne cewa ko yaushe Jamus na samun nasara a kan Ingila: Sau 15 Jamus ta lashe wasanni yayin da Ingila ta lashe sau 16.
1909: Wasan Jamus da Ingila mai cike da tarihi
Wannan shi ne wasa na hudu na kasa da kasa da kungiyar kwallon kafar Jamus ta buga kuma na biyu da Ingila, inda aka doke ta da 9-0 a Oxford. 'Yan kallo 6000 sun shaidar da kaye mafi muni da kungiyar DFB ta sha. Har yanzu masana tarihi suna jayayya game da kwanan wata. Domin a hukumance an gudanar da wasan ne a ranar 16 ga Maris. Amma ta yaya jaridu suka ruwaito cewa ya gudana a ranar 14 ga Maris?
1966: cin kwallo na uku a Wembley...
... Ba mu nuna a nan ba, amma an nuna shi sau da yawa. Kuma yanzu ya bayyana a fili cewa kwallan Geoff Hurst bai shiga ba. A wasan karshe na cin kofin duniya na 1966 a Landan, dan wasan baya Wolfgang Weber (a hagu a layin kasa) ya tilasta karin lokaci bayan 2-2 a minti na 90. Sauran bayanan sun shiga cikin tarihi. Ingila ta lashe bajinta mafi girma da ci 4-2 a gaban Jamusawa da ke cike da takaici.
1968: Nasarar Jamusawa ta farko
An shafe tsawon shekaru 59 da wasanni 13 kafin Jamus ta yi nasara a kan Ingila a karon farko. Franz Beckenbauer na Hannover ne ya ci kwallon nasara don daukaka kasarsa da 1-0? Bisa ga wadanda suka shaida wasan, ya kasance karon batta mafi daukar hankali tsakanin abokan adawar guda biyu. A karshe dai, a gaban 'yan kallo 80,000, wannan nasarar ta zama ramuwar gayya mai kima.
1970: Buga kwallo da kai da Seeler ya yi
Tawagar Jamus ta kasance a baya da ci 2-0 a zagaye dab da na karshe a gasar cin kofin duniya a Leon ta Mexico lokacin da Franz Beckenbauer da kuma kyaftin Uwe Seeler suka hada karfi. Seeler (daga dama) cikin wayo ya buga kwallon da gefen kai zuwa ga mai tsaron gida Peter Bonetti. Amma bayan da aka kara lokaci, Gerd Müller ya bayar da damar zuwa wasan kusa da na karshe da Italiya.
1972: Mafi kyawun kwallon na kowane lokac
"Ba za a samu wani sauyi a wannan nasarar ta 3-1 ba," Wannan shi ne furuncin Paul Breitner bayan nasarar farko ta wata kungiyar 'yan kwallon Jamus a Wembley. Abokan wasansa Uli Hoeneß, Günter Netzer da Gerd Müller ne suka zira kwallayen. Sai dai a wata-fainal na gasar Turai, akwai wasanni da suka rage. Amma makonni biyu bayan haka aka yi 0-0 ya biyo a Berlin - daga bisani Jamus ta lashe kofin.
1982: Babu yabo a gasar Spain
A shekarar 1982, an fuskanci kalubale a wasanni tsaka-tsaki a gasar duniya. Ana da Jamus da Spain da Ingila a rukuni daya. Amma tashi 0-0 da Ingila, ya sa 'yan wasa Manfred Kaltz, Ulli Stielike da Hans-Peter Briegel sun kirkiro da kyakkyawan tsari, wanda ya sa su kayar da Spain da ci 2-1 kuma suka kai wasan karshe ta bugun fenareti a kan Faransa . Amma dai Italiya ce ta ci 3-1.
1990: Lokacin da reshe ya fara juyewa da mujiya
Gary Lineker na Ingila cikin takaici ya ce "A ka'ida, kowace kungiya za ta iya doke kowace kungiya a bugun fenareti, sai dai in Ingila za ta buga wasa da Jamus." Sai dai Stuart Pierce (hoto) da Chris Waddle sun nuna jijiyoyin wuya su a wasan kusa da na karshe na cin kofin duniya, yayin da 'yan wasan Jamus suka yi bugun fenariti da ci 4-3 a tsanake.
1996: Mun je garinku mun fi ku rawa
An yi tsammanin cewa wannan zai zama dama ta biyu ga Ingila, domin ta kai wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin Turai da ke gudana a cikin kasar. Amma Jamus ce ta zama abokin hamayyarta, kuma bayan 1:1 a minti 90 na wasa da karin lokaci - an kai ga bugun fenareti. A wannan karon Gareth Southgate ya gaza cin Andreas Köpke - yayin da Andreas Möller (hoto) ya zira kwallo.
2000: Didi ya rusa lissafin Ingila
Wannan shi ne wasa na karshe a filin wasa Wembley kafin a sabunta. A wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Turai, masu masaukin bakin suna son yin ban kwana da filin wasan tare da yin nasara a kan Jamus kafin a rushe tare da maye gurbin sa da na zamani. Amma Didi Hamann na Jamus (Lamba 10) ya rusa wannan lissafin. Ya zira kwallon daya, lamarin da ya sa aka tashi wasan 1-0.
2001: Owen ya zira kwallo sau uku
Wannan shi ne abin da ake kira gagarumar nasara: Lokacin da Jamus ta yi zarra a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya sakamakon kwallon da Carsten Jancker ya zira, Ingila ta fara kai kora. Daga nan ne Michael Owen (Hagu.), Steven Gerrard (dama) da Kuma Emile Heskey suka yi ta gasa wa Jamus aya a hannu da ci 5-1. Owen ya zira kwallo sau uku.
2010: Ramuwar gayya a wasan Wembley
A minti 40 na zagayen bayan wasannin rukuni na kofin duniya a Afirka ta Kudu, Jamus na doke Ingila da ci: 2: 1. Daga nan Paul Lampard ya buga kwallo da kowa ya gan shi a cikin ragar Jamus. Amma alkalan wasa ba su gani ba! Daga bisaniThomas Müller ya karu zira kwallaye biyu, wanda ya sa aka tashi 4-1, lamarin da ya sa aka tuna da wasan da ya gudana a Wembley '66 ...
2013: Nasara ta shida a jere ga Jamus
Wasan sa da zumunci ne kawai, amma wasa a Wembley na da wata daraja a ko yaushe. ci 1-0, da dan wasan Ingila Per Mertesacker (hoto) ya zira, ya kawo nasarar ta shida ta Jamus a jere. Kuma wannan, duik da cewa babban kocin Joachim Löw ya dama ba tare da gudunmawar 'yan wasa kamar Manuel Neuer, Philipp Lahm, Bastian Schweinsteiger ko Mesut Özil a wasan karshe da Ingila ba.
2016: Ramuwar gayya ta Ingila a kan Jamus
Kowa ya yi zaton cewar Jamus za ta lashe wasan cikinn sauki. Toni Kroos da Mario Gomez na Jamus ne suka sa masu masaukin bakin kwallaye biyu. Amma a cikin mintuna 30 na karshe, kungiyar ta Jamus ta bayyana raunin da yawa. Harry Kane, wanda ya maye gurbin Jamie Vardy da ya jefa kyakkyawan kwallon da kafa (hoto) da Eric Dier suka juya wasan da Ingilishi ta samu nasara.
2017: 'Yan Ingila sun kosa da salon wasa
A haduwa ta karshe tsakanin kasashen biyu, kungiyar ta Jamus ta samu damammaki da yawa. Godiya ta tabbata ga dan wasan gaba Leroy Sané, saboda bajintar da ya nuna. Sai dai wasan gwajin dafin ya kare babu ci. Bayan dawowa hutun rabin lokaci, wasan ya zama marar sha'awa, har ya sa magoya bayan Ingilishi yin laushi da jiragen takarda. Watakila ba za a fuskanci wannan a Gasar Turai ba.