Karuwar hare-hare a Niger Delta
June 1, 2016
Wannan harin dai ana iya cewar na takwas kenan, wadda kuma ke yin mummunan tasiri kan ayyukan mai a kasar ta Najeriya. A baya bayanan ne dai hukumomi a kasar suka sanar da isar kayayyakin aiki na dakarun tsaro a yankin na Niger Delta don tunkarar 'yan binddgar da ke kai wadannan hare-hare. Wannan sabon harin na yau Talata da ya tarwatsa wadannan manya-manyan rijiyoyin na mai masu lambobi RMP 23 and RMP 24 na kamfanin na Chevron. Bayanai sun tabbatar rijiyoyin na daya daga mahimman rijiyoyin aikin hakar man kamfanin.
Harin dai ya afku ne a karamar hukumar Warri ta arewa da ke jihar Delta, kuma ya na daya daga jerin hare-hare da kungiyar Niger Delta Avengers ta ke ci gaba da kaiwa da kuma ta ke lasar takwabin tsananta munin wadannan hare-hare da nufin durkusar da harkokin mai a kasar ta Najeriya. Bisa dai la'akari da wannan hari na yau, za'a iya cewar adadin hare-haren da kungiyar ta Niger Delta Avengers din ta kai a kan kadarorin kamfanonin mai na kasashen ketare da kuma ma na gwamnatin Najeriya wato NNPC sun kai kimanin takwas.
Wani da ke da kusa da tsagerun da ke dauke dauke da makamai a Niger Delta me suna Uropa, ya fadawa DW cewa "bisa dai abinda ni na sani yayin da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ke barin mulki, ya shawarta wa shugaba na yanzu Muhammadu Buhari cewar ya kula da tsaffin 'yan bindiga irin su Tampolo da sauransu. Don ci gaba da cimma daidaito na yankin na Niger Delta, amma sai daga bisani akai yi watsi da haka, sakamakon shawarwarin wasu da aka bi. Amma dai shugaba Muhammadu Buhari ya na da akida mai kyau, kuma shugaba ne na kwarai. Sai dai akwai shawarwarin wasu da ba lallai su yi amfani ba kuma wannan hare-hare za su ci gaba sai dai abinda hali yayi"
Tuni dai gwamnati ta auno wasu jiragen sama na yaki hudu da kuma jiragen yaki na ruwa kimanin 100 don tunkarar wadannan yan mayakan masu kassara ayyukan mai a yankin na Niger Delta. To ganin cewar wasu na hangen akwai siyasa a cikin dambarwar da ke faruwa yanzu ta 'yan bindiga a wannan yanki, wasu mutane irinsu Injiniya Ma'azu Magaji wani tshohon ma'aikacin kamfanin mai na Shell suna yin sharhi kamar haka. Kafin dai a kai wannan hari na yau Talata, adadin gangar danyan mai miliyan daya da dubu dari daya, kasar ke hakowa kullum maimakon ganga miliyan biyu da dubu dari hudu a kullum din a da.
Wasu bayanai na nuna cewar, babu wasu alamu na cewar za'a kawo karshen wadannan hare-hare na kungiyar ta Avengers cikin wani zaman tattaunawar sulhu, face ga dukkanin wasu tanade-tanade da ke kasa, fito na fito ne kawai za'a ci gaba da yi. Akwai dai rahotanni da bana hukuma ba, da ke nuna cewar ana samun salwantar rayukan jami'an tsaro da na yan bindigar a fafatawar da ake yi.