1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin shiga nahiyar Turai ta barauniyar hanya

Binta Aliyu Zurmi
October 13, 2022

Hukumar hadin gwiwa ta Frontex da ke kula da tsaron kan iyakokin kasashen kungiyar tarayyar Turai ta ce, a watanni 9 na wannan shekara an sami karuwar mutanen da ke yunkurin tsallakawa nahiyar ta barauniyar hanya.

https://p.dw.com/p/4IA65
Griechenland | Flüchtlingslager in Kos
Hoto: Aris Messinis/AFP

Hukumar ta Frontex ta ce da sama da kaso 70 cikin dari aka sami karuwar masu kokarin shiga Turai idan aka kwatanta da wannan lokacin a shekarar da ta gabata.

A watan Satumba kadai hukumar ta yi rajistar sama da mutum dubu 33, inda ta ce dubu 19 sun fito ne daga kasashen yankin Balkans, yayin da wasu da suka fito daga bangaren tekun Bahar Rum suka hada da 'yan kasashen Siriya da Najeriya da ma kasar Kwango.

Wannan adadin shi ne mafi yawa da aka samu tun daga shekarar 2016. Hukumar ta ce yanzu haka sun kai makura a adadin da suke iya dauka.

Yin kaura ta barauniyar hanya zuwa nahiyar Turai na karuwa sabili da tashe-tashen hankula da ma matsaloli na tsaro da kasashen duniya da dama ke fama da shi.