Kasar Brazil ta haramta amfani da shafin X
September 1, 2024Kungiyoyin da ke rajin kare hakkin 'dan Adam na kallon matakin na mahukuntan Brazil din a matsayin wani yunkuri tauye 'yancin fadar albarkacin baki ta kafafen sadarwar zamani.
Karin bayani: Brazil: Kotu ta haramta wa Bolsonaro damar mulki
Toshe shafin a X a kasar ta Brazil dai ya biyo bayan hukuncin da kotun kolin kasar ta zartar, karkashin jagorancin mai shari'a Alexandre de Moraes, bayan da aka bude wasu shafukan X da alkalan kotun suka haramta amfani da su tun da fari.
Karin bayani:Brazil: Lula ya sha alwashin yakar rashawa
Baya ga Brazil wasu kasashen sun sanyawa al'ummarsu takunkumi na wucin-gadi ko kuma na dindindin wajen amfani da shafin na X, wadannan kasashe sun hada da Masar a lokacin guguwar sauyin kasashen Larabawa a 2011, da kasar Turkiyya a 2014 da kuma 2023 sai kuma kasar Uzbekistan a yayin zaben shugaban kasar a shekara ta 2012. Sauran kasashen sun hadar da Chiana da Turkmenistan da Iran da dai sauransu.