Kasar Kenya ta nuna bacin ranta ga kasashen G8
January 11, 2006Mahukuntan kasar Kenya sun bayyana rashin jin dadin su ga kasashen G8 ,a game da kin saka sunan kasar a cikin jerin kasashen da za´a yafewa bashi.
A cewar ministan kudi na kasar, wato David Mwiraria da alama kasashen na G8 sun yi hakan ne da gangan don ladaftar dasu a game
da kyakkyawan ci gaba da kasar ta samu a fannin tattalin arziki.
A cewar ministan dinbim bashin da kasashen na G8 suke bin kasar ta kenya na daya daga cikin matsalolin kasar na rashin samun ingantaccen tattalin arziki a kasar.
A karshe ministan ya tabbatar da cewa, wasu daga cikin kasashen da aka tsara yiwa yafiyar , kasar ta Kenya tafi su matsaloli dake da nasaba da tattalin arziki.
A dai shekarar data gabata ne, kasashe masu arzikin masana´antu na duniya da aka fi sani da suna G8 a turance suka bayar da sanarwar yafewa wasu matalautan kasashe dimbin bashin da suke bin su.