Taron koli kan sauyin yanayi a Kenya
September 4, 2023Taron zai mayar da hankali kan hanyoyin da za a bi don mayar da nahiyar Afrika babbar cibiyar samar da makamashi mai inganci tare kuma da mika kokon bara don neman tallafi daga kasashen duniya domin taimaka wa shirin.
Karin bayani: Sarrafa hikimomi ta hanyar amfani da hasken rana
A tsawon kwanaki uku shugabannin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da masu ruwa da tsaki kan sauyin yanayi ciki har da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres za su samar da shawarwari na bai daya da nahiyar Afrika za ta gabatar a taron koli na duniya kan sauyin yanayi na COP28 wanda za a gudanar a Hadaddiyar Daular Larabawa a karshen watan Nowamba mai zuwa.
Karin bayani: Masar: Taron sauyin yanayi na duniya COP27
A karshen taron, kasashen Afrika 54 za su fitar da daftari domin jaddada mahimmancin nahiyar wajen zama muhimmin bangare inda ya kamata a karkata domin samun mafita kan dumamar yanayi da ke addabar duniya.