Nijar da Mali da Burkina Faso sun fice daga ECOWAS
January 28, 2024Talla
Gwamnatocin kasashe uku na yankin Sahel da ke karkashin jagorancin sojoji da suka hada da Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso, sun sanar da ficewa daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ko CEDEAO.
A cikin sanarwar hadin gwiwar da aka karanto a gidan talabijin na kasar Nijar, kakakin majalisar mulkin soji a Njiar, Kanar Amadou Abdrahmane ya ce, bayan shekaru 49, masu kishin Burkina Faso da Mali da Nijar na takaicin ganin cewa kungiyar ECOWAS na kaucewa manufofin wadanda suka kafata don ci-gaban yankin.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, kungiyar ta gaza taimakawa wadannan kasashen a yankin da suke fama da ta'addanci da ma rashin tsaro.