Kasashen da ake magana da Jamusanci
Ana magana da harshen Jamusanci a wasu kasashen duniya 45. A wadanne kasashen aka fi samun masu magana da harshen Jamusanci?
Jamus da Ostiriya da kuma Liechtenstein
Kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU guda uku da ake amfani da harshen Jamusanci a hukumance: A dan karamin yankin Liechtenstein, kimanin mutane dubu 35 ke magana da Jamusanci; Ostiriya na da kimanin mutane miliyan bawaki da dubu 500 da suke Jamusanci sai kuma uwar gayya Jamus da ake magana da harshen a fadin kasar, ko da yake ba gaba daya al'ummar kasar wajen miliyan 83 ne ke yin Jamusanci ba.
Switzerland
A Switzerland, Jamusanci na cikin harsuna hudu da ake amfani da su a hukumance a kasar. KImanin kaso biyu bisa uku na al'ummar kasar miliyan biyar na yin Jamusunci. Akwai 'yan ci-rani daga Jamus kamar Hermann Hesse da Erich Maria Remarque da suka kasance fitattun marubuta.
Luxemburg
A Luxemburg ma, Jamusanci na cikin harsunan da ake amfani da su a hukumance a kasar tare da yaren Luxembourgish da Faransanci. Kimanin mazauna kasar dubu 470 na magana da Jamusanci a matsayin harshen uwa. An fara amfani da harshen Luxembourgish a hukumance a shekarar 1984, kuma mafi akasari ana amfani da shi ne a gidajen radiyo da talabijin. Mafi akasari, ana amfani da Jamusanci wajen rubutu.
Faransa
Bazuwar yare, na nuna asali: A Faransa Jamusanci yare ne na 'yan tsiraru. Masu magana da harshen Jamusanci a kasar su miliyan daya da dubu 200, na zaune ne a yankunan da ke kan iyakar kasashen Jamus da Faransan da suka hadar da Alsace da Champagne-Ardenne da kuma Lorraine. Akwai tsofaffin yanayin rubutu da ke tunatar da lokacin shugabancin Jamus.
Italiya
Jamusanci ne harshe mafi karanci da ake amfani da shi a hukumance a kudancin Tyrol da ke Italiya, yankin da ke karkashin kasar Ostriya har zuwa shekara ta 1919. Har kawo yanzu, kaso sama da 60 cikin 100 na mazauna yankin Bolzano da ke kudancin Tyrol, yankin da ke da yawan al'umma dubu 520, na amfani da Jamusanci a matsayin harshen uwa. A yankin ana rubuta alamomi da Jamusanci da kuma Italiyanci.
Spain
A nahiyar Turai, Spain ta fi daukar hankulan 'yan ci-rani daga Jamus. KImanin Jamusawa dubu 500 na zaune a Spain. Jamusawa da dama sun mamaye Tsibirin Canary da Mallorca da kuma gabar ruwan Spain. Wadannan yankunan na kuma jan hankulan masu yawon bude idanu daga Jamus.
Holland
A garuruwan Holland da dama kamar garin Venlo (da hotn sa ke sama), ana magana da harshen Jamusanci kuma ana amfani da shi a rubuce bayan harshen da ake amfani da shi a hukumance. Kimanin Jamusawa dubu 360 da suka yi kaura ke zaune a Holland. Makarantun kasar ta Holland da dama, na koyar da harshen Jamusanci a matsayin bakon yare.
Ireland
Jamusawa sun bar alamominsu a yankunan kasar Ireland. Kwararren mai zanen Jamus Richard Castle ne ya zana gine-gine da dama a birnin Dublin a farkon karni na 18. A yanzu akwai kimanin mutane dubu 100 da ke magana da Jamusanci a Ireland.
Isra'ila
Kimanin Isra'ilawa dubu 100 na magana da harshen Jamusanci; da daman su suna da asali da Yahudawan da suka yi gudun hijira. A baya dai Jamusanci ya wahala, inda ake masa kallon yaren 'yan Nazi. Kimanin shekaru 20 da suka gabata, hakan ta kau. Kamar yadda ake samun karuwar sha'awar hulda da Jamus, haka ake samun karuwar sha'awar yaren. Wasu makarantu na koyar da Jamusanci a matsayin bakon yare.
Rasha
Jamusanci a Rasha ya samo asali ne daga tarihin sama da shekaru 250. A shekara ta 1763, sarauniya Catherine ta biyu wato Catherine the Great haifaffiyar Jamus, ta kyale manoma su zauna a Volga. Bayan shekara ta 1990, da dama cikin kimanin Jamusawa Rashawa miliyan biyu da dubu 300, sun koma Jamus. A yanzu kimanin Rashawa masu asali da Jamus dubu 394 na zaune a Rasha. Ba dukka ke jin Jamusanci ba.
Afirka ta Kudu
Afirka ta Kudu ta yi fice a kasashen Afirka, wajen karbar Jamusawa 'yan ci-rani. Kaso daya bisa hudu na mazauna birnin Cape Town Jamusawa ne. A nai wa wajen lakabi da Sauerkraut Hill. An kiyasta cewa akwai Jamusawa kimanin dubu 100 zuwa dubu 500 da ke zaune a kasar.
Amirka
Kusan Amirkawa miliyan 50 na ikirarin tsatson Jamusawa, kuma har kawo yanzu, ba dan bullar annobar coronavirus ba, Jamusawa kimanin dubu 10 ke barin kasar duk shekara, su je su zauna a Amirka. Kiyasi ya nunar da cewa a yanzu, kimanin mutane miliyan daya da dubu 100, na magana da harshen Jamausanci a Amirka. "German Belt," ya fara daga Alabama zuwa tsakiyar yammacin Montana da Wyoming da Colorado.
Kanada
Kanada ma ta yi fice sossai wajen karbar 'yan ci-rani. Sama da Jamusawa dubu 400, sun yi hijira zuwa Kanada tun daga shekarun 1940. Kimanain mutane dubu 430 na magana da harshen Jamusanci a Kanada. Lunenburg da aka samar a karni na 18, na zaman tsohon wuri da Jamusawa suka ya da zango a Kanada. Garin na gabar ruwa da ke Nova Scotia an sanya shi a kundin tarhi na duniya na UNESCO tun 1995.
Brazil
Kaso 10 na al'ummar Brazil na da tsatso da Jamusawa, wadanda suka yi kaura zuwa Brazil sakamakon talauci da sauran matsaloli na zamantakewa a karni na 19 da kuma karni na 20. Kimanain mutane miliyan daya da dubu 100 na magana da harshen Jamusanci a Brazil.
Ajantina
A kashin farko na karni na 20, Jamusawa sun kai yarensu zuwa kasashen da dama na Amirka ta Kudu da kuma ta Tsakiya. Kiyasi ya nunaar da cewa a yanzu haka kimanin mutane dubu 400 ke magana da harshen Jamusanci a Ajantina.
Namibiya
Duk da cewa Jamus ta taba yi wa Namibiya mulkin mallaka, kimanin mutane dubu 20 ne kacal cikin al'ummar kasar miliyan biyu da dubu 500 ke magana da Jamusanci a yanzu. Har yanzu akwai alamun yaren, misali zauren wasanni na Lüderitz, birnin da aka sakawa sunan wani dan mulkin mallaka. Baya ga haka, ana magana da Jamusanci a kasashe 45 a duniya, mutane 100 na magana da yaren a Papua New Guinea.