1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya na gudanar da taro kan magance yunwa

June 12, 2013

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da nasarar da kasashe ke samu na kawar da yunwa.

https://p.dw.com/p/18oLZ
Hoto: picture-alliance/dpa

Kusan kasashe 40 na duniya sun hallara a birnin Rome na kasar Italiya, domin gudanar da taro gabanin lokacin da aka yanke na kawar da yunwa a duniya zuwa shekara ta 2015.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da abinci, ta ce daga shekarar 1990 zuwa shekara ta 2015 kawar da yanwu na cikin burin da aka saka a gaba, kuma yana daya daga cikin maradun karni. Ya zuwa shekara ta 2012 kasashe masu tasowa da dama sun dakile yunwa cikin kasashen da rabi.

Ranar Lahadi mai zuwa hukumar ta abinci za ta girmama kasashe da suka taka mahimmiyar rawa wajen magance matsalar ta yunwa, a bikin da za a gudanar a helkwatar hukumar da ke birnin Rome na kasar Italiya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman