Kasashen Larabawa sun katse hulda da Katar
June 5, 2017Kasashen Saudiyya da Masar da Baharain da kuma Daular Larabawa sun sanar da katse huldar diplomasiyyarsu da kasar Katar a bisa zarginta da tallafa wa ayyukan ta'addanci da kungiyoyin 'yan ta'adda da suka hada da Al-Qaida da IS da Kungiyar 'Yan uwa Musulmi da ma yin katsalandan a cikn harkokin cikin gidansu.
Kazalika an kori kasar ta Katar daga rundunar kawancan kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta a yakin kasar Yemen. Wannan rugum da ya faru a fagen diplomasiyyar kasashen na Larabawa ya zo ne kwanaki 15 bayan ziyarar da Shugaba Trump na Amirka ya kai a birnin Riyadh inda ya bukaci kasashen Musulmi da su dauki kwararan matakai wajen yaki da kaifin kishin Islama.
Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya na SPA ya ruwaito cewa ko baya ga katse huldar diplomasiyyar da kasar Katar, Saudiyyar ta kuma sanar da rufe iyakokinta na kasa da na sama da Katar domin abin da ta kira kare kanta daga barazanar ta'addanci da kuma tsattsauran ra'ayin addini.