kasashen Musulmi na taro a Istanbul
April 12, 2016Talla
Ziyarar Sarki Salman na Saudiyya na zuwa ne a daidai lokacin da ministocin kungiyar kasashen Musulmi ta duniya OIC ke gudanar da wani taro a Istanbul.Sarki Salman na Saudiyya tare da tawagarsa za su gudanar da wasu jerin tattaunawa kafin daga bisani su wuce kai tsaye babban taron OIC da ake gudanarwa yanzu haka a birnin Istanbul.
A yayin fara taron sai da ministan harkokin wajen Turkiyan Mevlut Cavusoglu ya shaidawa duniya cewar: "A matsayinmu na al'ummar Musulmi a duniya lokaci yayi da ya kamata mu dakatar da abubuwan da ke faruwa a Syriya, ya zama wajibi mu yi duk abin da ya dace wajen dawo da zaman lafiya a Siriya, kana a fili take sauyin da ake bukatar samu ba zai yiwu ba a gwamnatin Bashar al-Assad."