Kona al-Qur'ani ya janyo cece-kuce
June 29, 2023Talla
Kasashen na Iraki da Iran da Saudiyya da kuma sauran kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, sun yi gargadin cewa kona al-Qur'ani a Sweden Salwan Momika mai shekaru 37 a duniya ya yi tayar da hankulan Musulmin duniya ne. 'Yan sanda a Stockholm sun bai wa Momika dan asalin kasar Iraki mazaunin Sweden din damar yin zanga-zanga karkashin 'yancin fadar albarkacin baki tare kuma da ba shi kariya, inda shi kuma ya tattaka tare da kona shafukan al-Qur'ani a gaban babban Masallacin birnin. Sai dai kuma daga bisani 'yan sandan sun ce, sun fara gudanar da bincike kan kokarin tayar da tarzoma da suka ce mutumin ya yi. Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da miliyoyin al'ummar Musulmi ke dab da kammala gudanar da aikin Hajjin bana a Saudiyya.