Kashe wani mai tsattsauran ra'ayi a Kenya
April 1, 2014Amirka da Majalisar Dinkin Duniya dai na zargin Abubakar Shariff da tallafawa kungiyar Al-Shabab ta Somaliya dake da alaka da al-ka'ida. Wani jam'in 'yan sanda ya nuna gawar tasa bayan da aka kashe shi a garin Mombasa dake kasar ta Kenya. Wakilin kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ya tabbatar da ganin gawar Abubakar Shariff a garin na Mombasa.
A nasa bangaren Lauyan marigayi Abubakar Shariff, Attorney Mbugua Mureithi ya ce an kashe shi ne har lahira. Kawo yanzu babu wani cikakken bayani daga rundunar 'yan sandan kasar Kenyan kan mutuwar tasa. Dama dai tun da farko rundunar 'yan sandan kasar ta sanar da cafke sama da muatane 650 bisa zarginsu da hannu kan wani harin ta'addanci da aka kai a kasar a baya-bayan nan.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar