1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta shiga kasuwnci mara shinge na Afirka

Gazali Abdou Tasawa
July 7, 2019

Najeriya da Benin sun sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci mara shinge tsakanin kasashen Afirka, a taron kolin kungiyar Tarayar AFirka AU da ke gudana a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/3Lhuc
AU Gipfel in Addis Ababa 2013
Hoto: Getachew Tedla HG

Zauren taron dai ya kece da tafi a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da takwaransa Patrice Talon na Jamhuriyar Benin suka sanya hannu kan yarjejeniyar a gaban sauran takwarorinsu na Afirka. Najeriya da Benin da Iritiriya na daga cikin kasashen da suka jima suna nuna dari-dari ga shiga wannan yarjejeniyar cinikayya mara shinge, wacce ta kunshi mutane miliyan 1,200. 

A yanzu dai daga cikin kasashen nahiyar ta Afirka 55, kasar Iritiriya ce kadai ba ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya cinikayyar ba, wacce ke da burin bunkasa huldar kasuwanci a tsakanin kasashen nahiyar Afirka.

Mutane kimanin dubu hudu da dari biyar ne da suka hada da shugabannin kasashe 32 da ministoci sama da 100 ke halartar taron na birnin Yamai, wanda zai kawo da kaddamar da wannan yarjejeniyar cinikayya ta Afirka.