Hagia Sophia na kan hanyar zama massalaci a Turkiyya
July 10, 2020Talla
Wasu kungiyoyi da dama ne a kasar Turkiyya suka shigar da kara a gaban kotu, suna masu kalubalantar hukuncin shuwagabannin kasar na wancan lokaci karkashin jagorancin Mustafa Kemal, na mayar da wurin a matsayin gidan kallo da tarihi a 1934, shekaru bayan ya yi zama a matsayin wurin ibadar musulmi a yayin mulkin daular Ottomans a 1453.
Hagia Sophia ko Sainte-Sophie dai, na daga cikin wuraren tarihin da ke karkashin kulawar hukumar ilimi da raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, kana kuma ko a shekarar bara kawai akalla mutum fiye da miliyan 3.8 ne suka ziyarci wurin.