katangar Bagadaza domin raba alumomin sunni dana Shiá
April 22, 2007Talla
Amurka ta fara gina wata katafariyar katanga domin raba alúmomin sunni dana shiá a Bagadaza babban birnin kasar Iraqi. Wani mai magana da yawun sojin Amurka Brigadier Janar John Campbell kuma babban kwamandan sojin a birnin Bagadaza yace manufar gina katangar shine domin tabbatar da tsaro a yankin wanda ya yi kaurin suna wajen tarzoma da tashe tashen hankula a tsakanin mabiya dariku. Tun a ranar 10 ga wannan watan na Aprilu hukumomin sojin suka fara gina katangar mai tsawon kilomita biyar. Shugabanin alúmomin sun koka da gina katangar wanda suka ce za ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin jamaár kasar. Sai dai kuma a waje guda wani janar din sojin Iraqi yace katangar zata kasance kariya ga ayyukan yan taádda.