Kayayyakin agaji sun fara isa Khartoum na Sudan
December 30, 2024
Manyan motoci 28 ne suka isa Jebel Awliya da ke Kudu da birnin Khartoum, kamar yadda sashen bayar da agajin gaggawa na wata kungiyar sa kai da ke gudanar da ayyukan agajin gaggawa a fadin kasar Sudan ya bayyana. Ayarin ya hada da tireloli 22 dauke da abinci daga Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP, da wata tirela daya daga Kungiyar likitoci ta MSF da kuma tireloli biyar dauke da magunguna daga Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF.
Karin bayani: Yunwa na kashe yara a Sudan in ji UNICEF
Jebel Awliya, na daya daga cikin yankunan kasar Sudan da ke fuskantar matsalar 'yunwa bayan da bangarorin da ke fada da juna suka toshe hanyoyin shiga yankin. Tun lokacin da aka fara yaki a watan Afirilun 2023 tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, babu abin da ya shiga ko fita ba tare da amincewar bangarorin biyu ba.
"An toshe hanyar shiga yankin saboda yanayin rikice-rikice," in ji wakilin UNICEF na Sudan Sheldon Yett, inda ya kara da cewa "an kwashe watanni uku ana tattaunawa don ganin an bar ayarin motocin sun shiga." Kungiyar sa kai ta ERR Volunteers ta shafe watanni tana shiga tsakani, inda ta jure barazana da tarzoma domin ta samu damar shiga yankin. Dama kimanin mutane miliyan 23 a kasar ne ke bukatar agajin gaggawa don fitar da su daga matsananciyar 'yunwa.
Karin bayani: Al'amura na kara tabarbarewa a Sudan
Mutane sun yi jerin gwano saboda suna karbar kayyakin agaji. Usman Reidah na hukumar WFP ya ce: “Wadanda suka fi bukatar agaji a duk fadin Sudan su ne wadanda ke killace a wadannan yankunan da yaki ya fi tsanani a ciki. Mun kwashe watanni muna magiya da tuntubar bangarori masu yaki, kafin mu samu shiga da tireloli dankare da abinci da magunguna 30. Muna kira ga duk wadanda ke da damar shigowa yanzu, ya gaggauta kawo agaji.”
Karin bayani: Sudan na samun ci-gaba a fannin kwallon kafa a yanayi na yaki
Rahotannin da kungiyoyi masu zaman kansu suka bayar na tabbatar da cewa, nan da watanni shida masu zuwa, muddin ba a dakatar da yaki a Sudan ba, kasar da ake wa lakabi da kwandon abincin kasashen Larabawa za ta tsunduma cikin annobar 'yunwa. Sai dai gwamnatin Sudan na ci gaba da musunta wadanan rahotannin, inda ta zargi kungiyoyin da kururuta batun 'yunwa don ba wa 'yan tawaye halarcin neman aagaji. Wannan ya jawo wa gwamnatin kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakkin bil'adama da suke zargin ta da yin rufa-rufa da kokarin boye gaskiyar irin mawuyacin halin da 'yan Sudan ke ciki, don cimma muradinta na siyasa.