Yadda cin hanci ke dakile sufurin jirgin ruwa a Kenya
October 6, 2022Duk da muhimmancin da take da shi, a tsawon shekarun da suka gabata, hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Kenya, KPA, ta shiga mummunan yanayi. Daga cikin ababen da ke addabar hukumar har da zargin manyan manajoji da karbar cin hanci da rashawa daga masu samar da kayayyaki zuwa zambatar masu sarrafa kayayyakin da ke amfani da tashoshin jiragen ruwan kasar.
Shugaban kasar Kenya William Ruto a yayin bikin rantsar da shi, ya mayar da muhimman ayyukan hada-hadar kudi ta tashar jiragen ruwa na Mombasa daga tashar jiragen ruwa na Nairobi da Naivasha, don yaki da cin hanci da rashawa da kuma kawar da komabaya na kwantenoni da jigilar kayayyaki a tashoshin ruwa na cikin gida.
Charles Nganga dan kasuwa ne da ke shigo da kayayyaki daga kasashen waje ya shaida wa DW cewa hukumar KPA na cike da cin hanci da rashawa wanda ake karba a wajen 'yan kasuwa irinsa.
Masu ruwa da tsaki a bangaren sufurin kasar sun kuma nuna damuwarsu kan yadda aka killace su da gangan daga jigilar kayayyakinsu, lamarin da ya sa mutane da yawa suka rasa aikin yi.
Ana yi wa tashar jiragen ruwa ta Mombasa da ke Kenya kirari d 'babbar kofar shiga yankin Gabashin Afirka', wanda ke yin hidima ga kasashe makwabta irinsu Yuganda, Ruwanda, Burundi, Sudan ta Kudu, Arewacin Tanzaniya, Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, Habasha da kuma Burundi da Somaliya.
Sai dai Gilbert Langat, Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Kenya, ya ce cin hanci da rashawa a hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Kenya ya shafi bangarori da dama, ba wai a tsakanin jami'an tashoshin jiragen ruwa kawai ba ne.