Yara da dama a Kenya na fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata. Wani lokacin ma 'yan uwan yaran ne ke yin wannan aika-aika. Mafi akasari a kan boye labarin, batun da kwararru ke cewar ya na yin tasiri mummuna ga wanda aka ci wa zarafin kana ya na kara karfin gwiwa ga wanda suke aikata laifin.