1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya da batun Ebola sun dauki hankali a nan Jamus

Umaru AliyuOctober 10, 2014

Ziyarar shugaban Kenya Uhuru Kenyatta a kotun ICC da ci gaban yaduwar Ebola a duniya suna daga cikin abubuwan da jaridun Jamus suka maida hankali kansu a wannan mako.

https://p.dw.com/p/1DSw2
Uhuru Kenyatta Kenia Präsident
Hoto: Reuters/Peter Dejong

A wannan mako jaridun sun duba al'amura da dama da suka shafi nahiyar Afirka. Jaridar Berliner Zeitung misali ta yi sharhi ne kan ziyarar da shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya kai kotun kasa da kasa a birnin The Hague, domin sauraron laifukan da ake tuhumarsa kansu game da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben kasar a shekara ta 2007. Jaridar tace Kenyatta ya je kotun ne domin kare kansa daga wannan zargi. Sai dai ya zama shugaban kasa mai ci na farko da aka gurfanar dashi gaban kotun na kasa da kasa domin ya amsa wani laifi. Uhuru Kenyatta ana zarginsa ne da laifin taimakawa wadanda suka hura wutar tashin hankali, mafi yawansu yan kabilarsa ta Kikuyu a kasar ta Kenya, jim kadan bayan zaben shekara ta 2007, da kudi da makamai, domin haddasa mutuwar mutane masu yawa a kasar.

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta tabo halin da ake ciki ne na yaduwar cutar Ebola ba ma a nahiyar Afirka ba, amma har ma tana neman zama cutar da ta gama duniya baki daya. Jaridar tace abin da wata da watanni ake tsoron aukuwarsa yanzu dai ya tabbata. Cutar Ebola tayi kaura ta tsallake nahiyar Afirka. Yayin da mutum guda ya rasa ransa daga wannan cuta a Amirka, a nan nahiyar Turai ma wata ma'aikaciyar jiyya a Spain ta mutu daga sakamakon kamuwa da cutar. Ya zuwa yanzu, inji wani rahoto na hukumr lafiya ta duniya, wato WhO, mutane akalla 6553 suka kamu da Ebola a yankin Afirka ta Yamma, inda kusan mutane 3000 suka mutu ya zuwa yanzu. Hukumar tace cutar ta Ebola ma ta tsunduma tattalin arzikin kasashen Guinea da Saliyo da Liberiya cikin wani mummunan hali.

Jaridar General Anzeiger ta nan Bonn a wannan mako ta duba halin da ake ciki ne a kasar Sudan Ta Kudu, inda tace rashin kwanciaar hankali a kasar yana taka rawa ba ma ga rayuwar mazauna cikinta ba, amma har da yan kasar dake zaune a ketare. Jaridar tace a karshen shekara ta 2013 ne mummunan rikici ya barke a kasar da tafi kankantar shekaru a duniya. Tun bayan wannan lokaci duk mai dan abin hannunsa, ko wanda yake mallakar paspo na kasashen yamma ya fice daga kasar. Ya zuwa yanzu, mutane akalla dubu 80 ne suka tsallaketa zuwa makwabciyar Yuganda. Tun kafin hakan mahukuntan Sudan Ta Kudu sun ja hankalin baki masu yawa daga ketare zuwa kasar domin zuba jari da neman aiki, sakamakon arzikinta na man fetur. To sai dai jaridar General Anzeiger tace duk da wannan arziki, Sudan ta Kudu kasa ce mai fama da talauci, wadda bata iya kula da al'ummarta balle yan kasashn ketare masu neman cin arzikin da take dashi.

Ebola Transportmaschine
Jigilar masu dauke da cutar Ebola daga Afirka zuwa TuraiHoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/D. Stinellis

A karshe jaridar Süddeutsche Zeitung tace da alamu gwamnatin Jamus ta rage yawan taimakon raya kasa da take baiwa nahiyar Afirka, kamar yadda wasu alkaluma da aka samu a wannanm ako suka nuna. Gaba daya, inji jaridar, taimakon na Jamus zuwa ga Afirka ya ragu a shekara ta 2013 da kashi 13.9 cikin dari. A wasu yankunan Afirka kudu da Sahara, taimakon na Jamus ya ragu ma da abin da ya kai kashi 17.4 cikin dari. Gaba daya a bara din, taimakon raya kasa da Jamus ta baiwa Afirka a shekara ta 2013 bai wuce na Euro miliyan dubu ukku ba.

Tare da wannan sharhi na jaridar Süddeutsche Zeitung zamu dakata, Ahmed gareka.