Kenya: Kotu ta daure 'yan kungiyar likitoci masu yajin aiki
February 13, 2017Talla
A tsakiyar watan Janairu ne dai kotun ta yanke wa 'yan kungiyar likitocin hukuncin daurin wata guda na kason jeka ka gyara halinka, inda ta basu mako biyu na su kawo karshen yajin aiki, muddin ba haka ba, za su yi wannan kaso na wata daya a gidan kaso.
Da safiyar wannan Litinin din ce dai gaban dumbun magoya bayansu aka fice da su ya zuwa gidan kaso. Yajin aikin likitocin na Kenya dai ya soma ne tun daga ranar biyar ga watan Disamba da ya gabata, inda akasarin mutane ke zuwa ga asibitoci masu zaman kansu duk kuwa da tsadarsu.
Likitoci akalla 5000 ne dai da ke kasar ta Kenya, ke neman a rubunya albashinsu har sau hudu daidai da yarjejeniyar da aka cimma kan wannan batu a shekara ta 2013 ba tare da an aiwatar da ita ba.