Gelingt der Neuanfang in Kenia?
April 9, 2013Yau Tara (9) ga watan Afrilu ya kasance rana mai cike da tarihi a ƙasar Kenya. Uhuru Kenyatta mai shekaru 51 da haihuwa ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasa na huɗu. Lokacin bikin rantsarwar da aka gudanar da babban filin wasannin da ke Nairobi, Uhuru ya riƙe da littafi mai tsarki a hanunsa tare da matarsa a gefen sa. Magoya baya dai sun yi kuwa suna ɗaga tutocin ƙasar yayin da sabon shugaban ke ɗaukar alƙawuran gudanar da ayyukan da suka wajaba a kansa a nan da shekaru biyar masu zuwa.
Ga al'ummar ta kenya dai, wannan ranar na nufin ƙarshen zaɓen da duk duniya suka sanyawa ido, domin shekaru biyar da suka gabata, lokacin da ta yi zaɓen shugaban ƙasa, an shiga wani yanayi na rikici wanda ya kai ga hallakar mutane fiye da 1,200, wasu ɗaruruwa kuma suka rasa matsugunnensu.
Tun kafin ya kama aiki gadan-gadan, sabon shugaban ƙasar zai iya fara ƙidayar nasarorinsa, kasancewar ya bada tasa gudunmawar wajen ganin ba a maimaita rikicin da ya ɓarke wancan lokacin ba. A yanzu haka, 'yan ƙasar sun sami damar tabbatar da kyakkyawar makoma, to sai dai burin da aka sanyawa Kenyattan yi yawa Haɗakar jami'yyun Kenyatta sun ɗauki babban alƙwari wanda ya haɗa da yaƙi da talauci, inganta tsaro, da kuma samar da ababen more rayuwa.
Tubali mai mahimmanci ga tabbatar da ɗorewar sabbin abubuwan da ƙasar zata ƙaddamar shine, bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasar dole a zaɓi gwamnatocin larduna 47, kuma a ganin Peter Oesterdiekhoff Jami'i a ofishin gidauniyar Freidrich Erbert da ke Kenya, wannan zai sauya matsayin iko a ƙasar.
" Cire iko daga tsakiya, ya kasance kan gaba a buƙatun al'umma lokacin da suka gudanar da sauye-sauye a kundin tsarin mulkin ƙasar. Wannan na nufin rage ikon 'yan majalisa da kuma raba madafun iko, domin al'ummar ta shafe shekaru tana neman a riƙa damawa da ita, idan kuma batu ne na yankinsu suna tattauna su iya cimma matsaya kana kuma su iya zuba jari a yankunansu"
Kenyatta na ɗaya daga cikin attajiran Kenya wannan kuma na nufin da shi da iyalansa sun mallaki filaye da yawa, da aka yi masa tambayar ko wannan zai yi karan tsaye ga gudanar da sauye-sauye a tsarin mallakar filayen ƙasar, shugaban hukumar kula da filayen Mohammed Swazui ya yi taka tsantasan wajen bada amsa
"Akwai dokar da ta kamata mu bi, akwai kundin tsarin mulkin da ya kamata mu mutunta, kuma a tunani na idan har aka sami abunda ya saɓawa doka, shine za'a sami matsala idan har aka bi tanadin doka, kuma arziƙinsu bai saɓawa dokar ba babu matsalar da zamu samu"
A waje guda kuma, idan har kundin tsarin mulkin na shekarar 2010 ta rage ikon shugaban ƙasa, babu laifi ke nan a yanayin da zai fara gudanar da ayyuka. Idan kuma ya ƙulla kyakkyawar dangantaka da jam'iyya, zai iya samun rinjaye a Majalisa, to sai dai ɗorewar wannan rinjaye ne dai akwai shakku, wato idan har haɗakar jami'yyar Kenyatta da ta mataimakin shugaban ƙasa William Ruto ta yi nasarar ɗorewa har ƙarshen wa'adinsu, domin Ruto ɗan ƙabilan Kalenji ne a yayin da Kenyatta kuma ɗan Kikuyu ne a dalilin haka, attajiran ƙabilar Kikuyu ka iya nunawa Ruto da jami'yyarsa banbanci.
Masharhanta na ganin cewa maƙasudin ƙulla wannan ƙawance shine domin su yi nasara su sami rigar kariya daga shari'ar da ake sa ran gudanar musu a kotun hukunta manyan laifukan yaƙi ta ICC da ke birnin Hague, inda ake zarginsu da take haƙƙin ɗan Adam, hasali ma shi ya sa sakamakon zaɓen bai sami karɓuwa ba wajen ƙasashen ƙetare. Macharia Munene, mallamin kimiyyar siyasa ne daga Jami'ar ƙasa da ƙasa ta Amirka da ke Nairobi:
"Shaidun ba su nan yanzu, zargin kan shi ma ba a kan wani bincike mai ƙwari ba ne kawai kan jita-jita ne, yanzu ma ana cewa kuskure ne saboda haka, akwai yiwuwar cewa kotun ta ICC zata janye wannan ƙara
Sa idon dai ya yi yawa kan Kenyatta kuma dangantakar shi da al'ummar ƙasa da ƙasa zai yi wuya, shi yasa zai yi ta fatan cewa rashin hujjojin da ake faɗa ya kasance gaskiya.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi