1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya ta daura damarar yakar ta'addanci

September 24, 2013

Hukumomin Kenya sun bayyana karbe ikon gidan da 'yan bindiga na al-Shabaab suka yi kawanya, tare da neman hadin kan kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/19mzy
Hoto: SIMON MAINA/AFP/Getty Images

Gwamnatin Kenya ta ce jami'an tsaron kasar sun karbi iko da ginin cibiyar kasuwanci da ke birnin Nairobi, sannan sun kubutar da daukacin wadanda 'yan bindiga ke garkuwa da su. Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 62, yayin da wasu kimanin 200 suka samu raunika.

'Yan siyasan kasar ta Kenya sun hada kai domin tunkarar wannan hali da kasar ta samu kanta a ciki, na hari da 'yan ta'adda na kungiyar al-Shabaab da ke Somaliya. Harin na cibiyar kasawanci ta birnin Nairobim, da ya yi sanadiyar hallaka mutane 62, ya zama mafi muni da kasar ta fuskanta cikin shekaru 15 da suka gabata. A shekarar 1998 fiye da mutane 200 sun hallaka bisa harin ta'addanci kan ofishin jakadanci Amirka da ke birnin na Nairobi.

Tsohon Firamnistan kasar Raila Odinga kuma jigon 'yan adawa, ya nemi 'yan kasar su hada kai domin tunkarar lamarin:

"A lokaci irin wannan dole mu hadu kai a matsayin mutane, wannan lokaci ya zama kwaji wa kasarmu. Abu ne da ya shafi hadin kan kasarmu."

Cikin watannin da suka gabata an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a Somaliya inda kungiyar ta al-Shabaab da ta kai hari ta fito. Tun bayan zaben Shugaba Hassan Sheikh Mohamud cikin watan Satumban shekarar da ta gabata ta 2012, ake samun zaman lafiya sannu a hankali, bayan kwashe fiye da shekaru 20 ana zaman kara zube.

Nairobi Kenia Terroranschlag Al-Shabaab Einkaufszentrum Westgate Mall
Hoto: picture-alliance/dpa

Tun shekara ta 2011 kimanin dakarun kasar Kenya 4,600 ke Somaliya domin tabbatar da harkokin tsaro. Kuma tun wannan lokaci ake samu hare-hare cikin Kenya, inda yanzu haka ya dauki sabon salo.

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka sun samu nasarori musamman na kawar da 'yan al-Shabaab daga mahimman garuruwa na Magadishu da Kismayo. Masana na ganin 'yan kungiyar sun rasa manyan birane amma da sauran rina a kaba. Kamar yadda Emmanuel Kisiangani na wata cibiyar kula da lamuran tsaro da ke birnin Nairobi ya bayyana cewa:

Nairobi Kenia Terroranschlag Al-Shabaab Einkaufszentrum Westgate Mall
Hoto: Reuters/Thomas Mukoya

"Sun rasa tacewa ne kawai a biranen Somaliya, suna rike da wasu yankuna. Amma sun rasa mahimman wurare kamar Mogadishu da Kismayo, duk da haka ina tunatin cewa suna da karfin da za su janye barna."

Yayin da al-Shabaab ke neman ganin Kenya ta janye daga cikin Somaliya, abin da ta bayyana a matsayin dalilan kai wannan hari na cibiyar kasuwancin birnin Nairobi, masana harkokin tsaro na ganin biyan wannan bukata babu ba shi da wani amfani. Musamman saboda yadda mayakan na al-Shabaab suka dauki Kenya a matsayin babbar abokiyar gaba.

Guido Steinburg na gidauniyar kimiya da siyasa na maira'ayin cewa:

"Ina tsammani an makara da daukan duk wani mataki na janye dakarun Kenya daga Somaliya."

Wannan hari da kungiyar al-Shabaab ta kai cibiyar kasuwanci birnin na Nairobi da ke Kenya, ya ritsa da 'yan kasashen ketere, kumma babban abin zuba ido a gani shi ne, yadda kasashen duniya za su tunkari lamarin na dakile harkokin ta'addanci tsakanin kasa da kasa, bisa rahotannin da ke cewa akwai mazauna wasu kasashen da ke cikin maharan.

Mawallafa: Suleiman Babayo/Zainab Mohammed Abubakar
Edita: Umaru Aliyu