Kenya ta gaza daukar wasannin 'yan Afirka
September 24, 2017Kasar Kenya ta rasa dama ta daukar nauyin wasannin zakarun da ke taka kwallo a nahiyar Afirka ta CHAN a shekarar 2018 mai zuwa. Hukumar da ke tsara wasannin na Afirka CAF ta ce kasar ta Kenya ta yi nauyin jiki a kokari na shirye-shiryen karbar bakuncin wasannin na nahiyar da zakaru daga kasashe ke halarta.
An yanke wannan hukunci ne a wani zama da manyan jami'ai na hukumar suka yi a birnin Accra na Ghana a ranar Asabar kana a wannan rana ta Lahadi a ka bude dama ga sauran kasashen da ke da sha'awar daukar nauyin wasannin na CAF da su gwada ta su sa'ar su nema, kuma a cewar hukumar kasashen da ke da muradi na da nan zuwa Lahadi mai zuwa su aika da bukatarsu, yayin da kasar da ta yi nasara za a bayyanata nan da makonni biyu.
An dai tsara buga wasannin ne tsakanin 12 ga watan Janairu zuwa hudu ga watan Fabirairu mai zuwa. Kamar Kenya ita Kamaru za a yi nazari kan shirye-shiryenta na karbar bakuncin wasannin a shekarar 2019.