SiyasaAfirka
An nada sabon babban hafsan sojan Kenya
May 2, 2024Talla
An nada Laftanar Janar Charles Muriu Kahariri a matsayin sabon babban habsan tsaron kasar Kenya, inda ya gaji tsohon babban hafsan Marigayi Francis Omondi Ogalla da ya rasu sakamakon hadarin karamin jirgin sama mai saukan ungulu tare da wasu hafsoshin soja guda 10.
Shugaba William Ruto ya bayyana sunan Laftanar Janar Charles Muriu Kahariri mai shekaru 62 da haihuwa, wanda yake rike da mukamun mataimakin babban habsa, inda yanzu aka daga-likafansa zuwa babban habsan tsaron kasar. Sannan Shugaba Ruto ya nada Manjo-Janar Fatuma Gaiti Ahmed a mastayin mace ta farko wadda za ta jagoranci rundunar sojan saman kasar ta Kenya.