1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya tana ci gaba da fuskantar hare-hare

June 17, 2014

Sabon hari ya yi sanadiyar hallaka kimanin 15 kwana guda bayan harin da ya hallaka kimanin 50 a kasar Kenya.

https://p.dw.com/p/1CJqE
Hoto: picture-alliance/dpa

Tuni kungiyar ta al-Shaabab ta tabbatar da cewa ita ke da alhakin sabon harin da ya hallaka mutane 15, kusa da garin Mpeketoni mai tashar jiragen ruwa da ke zama daya daga cikin wuraren da ake samun masu yawan bude ido.

Babu tabbacin idan maharan suke a halin yanzu, ko suna cikin Kenya, ko kuma sun sake komawa cikin Somaliya, saboda kilo mita 60 ke tsakanin wurin da aka kai harin da kuma kasar ta Somaliya. 'Yan sanda sun ce 'yan bindigan da suka kai harin, sun kasance wani bangaren na wadanda suka kai harin farko da ya hallaka kimanin mutane 50.

Mataimakin gwamnan lardin Lamu da aka kai wannan hari Eric Magu, ya ce akwai yuwuwar maharan sun tsere:

Mpeketoni Kenia Anschlag Massaker
Hoto: REUTERS

"Mahara fiye da 50 cikin manyan motoci biyu, kuma bayanan da nake samu daga wasu majiyoyi na cewa sun kona motocin da suka zo a ciki, sannan suka tsere ta cikin daji, saboda ban yi imani za su iya wucewa ta hanyoyi ba, saboda akwai jami'an tsaro kowani lungu da sako."

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Kenya ta tabbatar da kai sabon harin da ya hallaka mutane 15, inda ministan ma'aikatar Joseph Ole Lenku, ya yi alkawarin hukunta wadanda suke da hannu cikin lamarin.

Adan Wachu sakatare janar na kungiyar Musulman kasar, ya yi tir da hare-haren, sannan ya ce Musulmai da sauran mabiya addinai za su ba da goyon bayan da ya dace wajen dakile ta'addanci a kasar. Shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyatta ya daura alhakin abin da ya faru kan 'yan siyasan yankin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu